Wannan sako na Leah Sharibu daga hannun 'yan Boko Haram tuni ya kara farfado da fatar cewa yarinyar na raye.
Da ya ke zantawa da gidan talabijin na TVC mai taimakawa shugaban Nigeria kan labaru Garba Shehu ya ce jami'an tsaron farin kaya na nazarin sautin don tabbatar da sahihancin sa
Tuni mahaifin Leah, Mr. Nathan Sharibu ya gane muryar 'yar sa, kuma hakan zai taimakawa jami'an binciken wajen gaggauta fitar da sakamakon binciken su kan lamarin."
Kan wannan batu na jinkirin sako Leah, ministan labarun Najeriya Lai Muhammed ya ce masu yarjejeniya da 'yan ta'addan na yi kuma don tattaunawa da 'yan ta'adda abu ne mai sosa rai amma tabbas za su dage har sai yarinya ta koma hannun iyayenta.
In za a tuna yan Boko Haram sun koma Leah ne wai domin taki shiga addinin Musulunci bayan da suka sako sauran matan na Dapchi.
Shehun malamin Islama Abdullahi Bala Lau ya ce babu tilas a shiga addini.
Shin rashin barin addinin kirista ne ko ma dai wani abun daban, masu sharhi na ganin 'yan Boko Haram na amfana a wajen fansar matan da su kan sace da ko a ce rike su don zama garkuwa.
Hakanan sakon ka iya nufin 'yan ta'addan na nuna har yanzu su na nan da karfin su.
A saurari rahoton Nasiru Adamu El-Hikaya
Facebook Forum