Yayinda yake zantawa da Sashen Hausa Sanata Ali Ndume ya jaddada cewa bisa ga farin jinin da Shugaba Buhari yake dashi a Arewa ba zai fadi zabe ba.
Amma ya amince cewa a wasu jihohin da wadanda suka canza sheka suke da karfi ana iya samun cikas, jihohi irin su Kano inda Kwankwaso ke da mabiya da yawa da Kwara inda Dr. Bukola Saraki yake da bakin-fada-a-ji. Sai dai ko a jihar Kwaran abubuwa na tangal tangal, domin a jihar ne shugabannin PDP suka fice suka koma APC domin komawar da Dr Saraki yayi cikinta. Senata Ndumi yace zabe mai zuwa ne zai nuna gaskiyar abun da zai faru.
Sanata Ndume yace ko a Majalisar Dattawa akwai wasu 'yan PDP dake son komawa APC. Kazalika wasu ma da suka koma PDP din, suna tunanen komawa inda suka fito, domin sun soma ganewa cewa nda suka koman ba mafita ba ce.
Sanata Ndume ya ce canza sheka ba sabon abu ba ne domin kowane duk lokacin da zabe ya karato, hakan ya kan faru, musamman idan har an hangi cewa akwai abun da ya tare wa dan siyasa hanya. A cewarsa yawancin wadanda suka canza sheka suna da matsala da gwamnonin jihohinsu ne ko kuma da jama'arsu.
Akan Shugaban Majalisar Dattawa Dr. Bukola Saraki, Sanata Ndume na ganin shi ya jawowa kansa matsalar da ta sa ya fice daga jam'iyyar APC, saboda yana yi mata zagon kasa. Misali, a cewar Sanata Ndume akwai ayyuka da yawa a gaban majalisar daaka bari ba'a yi su ba. Bugu da kari ya rufe majalisar suka tafi hutu, aka bar wasu muhimman ayyuka da ake bukata cikin gaggawa.
A saurari hirar Haruna Dauda da Sanata Ndume domin karin bayani
Facebook Forum