Wasu Jami’an gwamnatin Amurka sun shaidawa wa majilisar dokokin kasar cewa ko kusa kasar Rasha bata yi shisshigi ba a zaben shugaban kasar Amurka ba wanda aka gudanar a shekarar data gabata, musammam da niyyar taimaka wa hamshakin mai kudin Donald Trump da zummar samun nasarar shugabancin Amurka, Domin ko jamniaan suka ce ba wata hujjar dake nuna cewa kasar ta Rasha ta canza kuriun da aka jefa a wannan zabe.
Tsohon shugaban hukumar tsaron cikin gida Jeh Johnson ya shaidawa kwamitin kula da bayanan sirri na majilisar wakilai, dake sauraren rawar da ake tuhumar kasar Rasha ta taka a zaben shugaban kasar Amurka ta yin shisshigi ga komfutoci a hedikwatar jamiyyar Democrat a nan Washington, Yace wannan yunkurin da ake tuhumar kasar ta Rasha na yin shisshigi bai cimma nasara ba domin konfutocin kasar Amurka sunfi karfin kassar tayi musu wanna kutsen.
A wuri daya kuma jami'an kasar ta Rasha sunyi tsokaci akan sabon takunkumin da Amurka ta kara sa mata, ta dakatar da yunkurin tattaunawar dake son ayi tsakani Mukaddashin ministan harkokin waje na kasar ta Rasha Sergei Ryabkov da karamin ssakataren harkokin waje Thoomas Shannon.
Ryakov yace yanayin da ake ciki bai bada damar ayi wata tattaunawa ba.
Sai dai ma'aikatar ta kasar waje ta Amurka ta bayyana takaicin na ganin an dage wannan tattaunawar da aka yi niyyar yi gobe juma'a.
Jamiaan ma'aikatan suka ce sunyi bakin cikin ganin yadda kasar ta Rasha ta yanke shawarar watsi da wannan damar nayin bayani akan abinda ke kawo wa kasashen biyu cikas a dangantakar su, inji mai maganada yawun ma'aikatar wato Heather Nueert, a cikin wata sanarwan da ya fitar.
Facebook Forum