Rahotani sun ce babban jami’in bincike na musamman, Robert Mueller da ke bincike kan ko shugaban Amurka Donald Trump yayi yunkurin hana doka ta yi aikinta, yana gudanar da wani bincike na daban kan kamfanoni da bankuna da ke mu’amala da sirikin shugaban, wanda ya kasance ‘daya daga cikin mai baiwa shugaban shawara.
Jaridar Washington Post ta fitar da rahotan jiya Alhamis cewa Mueller yana bincike akan harkokin da suka shafi kudi na Jared Kushner, wato sirikin Shugaba Trump.
Wasu rahotanni da aka fitar da baya baya nan sun nuna cewa Kushner ya gana da mutumin da ke shugabantar bankin kasar Rasha. Lauyoyin Kushner sun ce za su bada hadin kai kan binciken.
Da safiyar jiya Alhamis ne shugaba Donald Trump ya mayar da martani ta kafar Twiiter kan cewa mai bincike na musamman yana gudanar da bincike a kansa kan cewa yayi yunkurin hana doka ta yi aikinta.
A wani sako na biyu da y a aika akan Twitter shugaba Trump ya ce wannan wani bita da kulli ne da ba'a taba gani ba a tarihin siyasar Amurka.
Facebook Forum