Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Jami'an Tsaro Farar Hula Dake Yankunan Kan Iyakar Nigeria Sun Shirya Fafatawa da 'Yan Boko Haram


'Yan bangan Fararen Hulan JTF suna anfani ne da kulake da sanduna da makaman da aka sarafa cikin gida suna sintiri a kan titunan Maiduguri, Najerya.
'Yan bangan Fararen Hulan JTF suna anfani ne da kulake da sanduna da makaman da aka sarafa cikin gida suna sintiri a kan titunan Maiduguri, Najerya.

Kungiyoyin ayyukan sa kai na farar hula a Nigeria da a takaice ake kira "JTF", sun ci alwashin fafatawa da 'yan Boko Haram

Rundunar sojin Nigeria, da rundunar sojin sama, hadi da rundunar 'yan sanda a Nigeria, sun hada karfinsu waje guda domin suyi aiki tare, su zama tamkar 'Tsintsiya' madaurinki guda domin su yaki mayakan kungiyar Islama da aka fi sani da sunan Boko haram, kungiyar da ta shafe shekaru da dama tana addabar 'yan Nigeria.Amma kuma, hadin gwiwar kungiyoyin tsaro na farar hula da a takaice ake kira "JTF", sun bayyana cewar a zahiri,soja kadai ba zasu iya murkushe 'yan Boko haram ba. Idan har aka yi la'akkari da sabbin hare-haren ta'addancin da suka rika kaiwa sansanonin soja dake yankin Arewa maso gabashin Nigeria a ran biyu ga watan Disamba.Hakika mayakan farar hula sun taka rawar gani a gwabzawarsu da mayakan 'yan kungiyar ta Boko haram.

A Nigeria, ba kasafai ake daukan kungiyoyin sa kai dake dauke da makamai a Arewacin Nigeria, masu hatsarin gaske ba, amma fi daukarsu a zaman jarumai. Anji daga bakin daya daga cikin shugabannin kungiyar ta "JTF Farar hula" a jihar Borno, Aba Abji Kall na fadin cewa kungiyoyin sa kai farar hular an kafasu ne bayan da jama'a suka dandana kudarsu a hannun mayakan Boko haram duk da shekara da shekarun da Gwamnati tayi tana kokarin hana tashe-tashen hankula ba'a kai ga samun nasarar yin hakan ba.Aba Abji Kall yana mai cewa" sun sukurkuta mana halin zaman rayuwa, da na tattalin arzikin mu, mun kuma yi asarar rayukan 'yanuwan mu masu tyarin yawa, a ta bakin Said Kall.
XS
SM
MD
LG