Lura da yadda annobar corona ke kara tsananta a wasu kasashen waje inda aka fara samin bular wani sabon nau’in kwayar cutar ya sa hukumomin Nijer soma yunkurin tsaurara matakan riga kafi mafarin wannan kamfe da za a fara a yau talata 15 ga watan yuni kamar yadda ministan kiwon lafiyar al’uma Dr Iliassou Idi Mainassara ya bayyana a taron manema labaran da ya kira.
Tuni aka kebe wasu wuraren musamman domin gudanar da wannan aiki na tsawon mako 1 saboda haka aka bukaci al’umma ta baiwa likitoci hadin kai.
Daga lokacin gano mutun na farko da ya kamu da cutar corona a nan Nijer a watan maris na 2020 kawo jiya litinin 14 ga watan Yuni mutum 5452 aka bayyana cewa sun harbu da kwayar cutar a wannan kasa daga cikinsu 5172 suka warke yayinda a yanzu haka mutum 88 ke asibiti domin karbar magani kuma bayanan hukumomin kiwon lafiya sunce mutane 192 ne cutar ta covid 19 ta kashe a tsawon wannan lokaci saboda ake kara kiran jama’a a ci gaba da biyayya ga matakan riga kafi.
Domin karfafa zagayen farko na allurar riga kafin da aka kaddamar a ranar 28 ga watan maris din da ya gabata ne hukumomin lafiya suka shirya zagaye na 2 da ke somawa daga yau talata 15 ga watan Yuni.
Saurari cikakken rahoton a cikin sauti: