Hukumomin kiwon lafiya a jamhuriyar Nijar, sun bayyana shirin kaddamar da gangamin riga kafin cutar Sankarau, a gobe Talata 5 ga watan Maris. Domin riga kafin cutar sankarau a wani matakin dakile barazanar da cutar ke yiwa rayuwar yara kanana, kamar yadda rahotanni ke cewa an samu bularta a yankin Damagaram.
Yara sama da miliyan 6 ‘yan kasa da shekaru 7 da haifuwa, ake saran yiwa Allurar riga kafi a yayin wannan kamfe na tsawon kwanaki 7 da za a gudanar a illahirin jihohin kasar Nijar, da nufin dakile barazanar kwayar wannan cuta a wannan lokaci na shiga yanayin zafi. Dr. Rabi Souley ita ce shugabar ma’aikatar Shausawa ta kasa PEV.
Cutar sankarau wace ake jerawa a sahun cututtukan dake yiwa masu karar kwana kof daya, kan bar wasu yaran da tawaya iri-iri.
A cewar Dr. Maman Sani Mahaman, mahimmancin wannan kamfe din na gobe Talata 5 ga watan Maris ya sa hukumomin kiwon lafiya kiran jama’a, akan bukatar bada hadin kai don ceto rayuwar yara daga illolin cutar sankarau.
Rahotannin karshen makon jiya daga yankin Zandar na cewa an samu bular kwayar cutar sankarau a wasu kauyukan gundumar Mirriah har ma ta fara kisa a cewar likitoci.
Ga rahoton wakilin muryar Amurka a Yamai Sule Mumuni Barma.
Facebook Forum