Humkumoni jihar Diffa da ke Jamhuriyar Nijar, sun cafke matasa 46 da suka yi kaurin suna wajen ta da zaune tsaye a jihar.
Daga cikin ire-iren miyagun ayyukan da ake zargin matasan na aikatawa, akwai shaye-shayen miyagun kwayoyi da fyade da fashi da makami da fadace-fadace tsakaninsu da a wani lokacin ake samun rasa rayuka da dai saurensu.
Ana dai iya cewa, rashin aikin yi ne ya jefa matasan na jihar ta Diffa shiga a cikin kungiyoyin na ta da zaune-tsaye da ake kira palais, wadanda suka shahara wajen kwace da fashi da makami da fyade da shaye-shayen miyagun kwayoyi da fadace-fadace tsakaninsu ta hanyar amfani da makamai da dai saurensu.
Rikicin baya-bayan na matasan na palais shi ne wanda ya faru a wata unguwa da ta tattara ‘yan gudun hijira da ake kira Djori kolo, bayan matasan na palais sun kaiwa unguwar farmaki, al’amarin da ya janyo mayar da martanin matasan wannan unguwa.
Kamar yadda Malam Soumaila Mohamed shugaban ‘yan gudun hijira na unguwar ta Djori Kolo yayi mani karain bayani.
A yanzu haka jami’an tsaron jihar Diffa sun tsafke matasa 46 bayan faruwar wannan al’amarin, to sai dai a cewar Abatcha Elh Ari wani mazauni jihar ta Diffa,har yanzu akwai sauren rina a kada, domin a yanzu haka akwai kungiyoyin na matasan na palais kimanin 1.600 a jihar ta Diffa.
A nasa bangare hukumomin jihar Diffa sun sha alwashin daukar dukkanin matakan da suka dace domin dakile wannan al’amarin.
Korodji Dalla shi ne shugaban Majalisar mashawartan jihar Diffa.
Ana dai iya cewa, wannan al’amarin na bayyanar kungiyoyin na matasan a jihar Diffa, ya soma asali ne tun a shekarar 2015, bayan sakawa jihar dokar ta bace sakamakon rikicin boko haram,al’amarin ya jefa matasan jihar da dama cikin zaman kashe wando.
Saurari cikakken rahoton Aboukar Isa daga Diffa: