Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Jama'a Sun Takura Sosai A Jihar Adamawa Dalilin Dokar-Ta-Baci


Akasarin tituna wayam a Yola, babban birnin Jihar Adamawa, a sanadin dokar-ta-baci wadda ta takura harkokin rayuwar yau da kullum
Akasarin tituna wayam a Yola, babban birnin Jihar Adamawa, a sanadin dokar-ta-baci wadda ta takura harkokin rayuwar yau da kullum

Rashin hanyoyin sadarwa sun takura ma jama'a sosai a Jihar Adamawa, inda a yanzu sai jama'a sun yi gayya sun tafi zuwa wasu jihohyin domin su buga waya ga 'yan'uwa a wasu sassan Najeriya

Al'ummar Jihar Adamawa, daya daga cikin jihohi ukun da aka kafa dokar-ta-baci, sun ce babbar matsalar da suka fi fuskanta ita ce ta katse hanyoyin sadarwa da hukuma ta yi, wata guda da daukar wannan matakin da shugaba Goodluck Jonathan ya ayyana.

Wakilin Sashen Hausa, Ibrahim Abdulaziz, yace a yanzu, jama'a da dama daga Yola, babban birnin Jihar, da wasu sassan, su kan dauki hayar motoci da wasu ababen hawar zuwa wasu garuruwa da wurare a tsallaken iyaka a Jihar Taraba, domin su samu zarafin yin magana da 'yan'uwa ko abokan huldar cinikayyarsu a wasu sassan Najeriya da duniya.

Wasu kwararru kamar 'yan kwangila da malamai, su ma su na barin jihar a saboda wannan hali na rashin hanyar tuntubar 'yan'uwansu a kasashen waje. Gwamna Murtala Nyako, yace wannan lamarin ya shafi shahararriyar jami'ar nan ta ABTI-American dake Jihar, wadda malamanta suke barin gari a saboda halin da aka shiga.

Sai dai kuma a wani lamarin, wasu masu sana'a a irin garuruwan da mutane ke zuwa domin su yi wayar, sun bayyana wannan abu a zaman wani abin alheri a gare su, a saboda samun karin masu ciniki. Wata mai toyawa da sayar da doya ta ce a yanzu, tana samun kasuwa sosai a saboda dimbin jama'a dake zuwa.

'Yan jarida da dama su ma sun koka a saboda wahalar da suke samu wajen samo labarai ko aika su ga kamfanoninsu.

Ga cikakken rahoton Ibrahim Abdulaziz daga Yola, kan wata guda da shiga dokar-ta-baci a Jihar Adamawa.

Wata Guda Da Dokar-Ta-Baci, me Ke Faruwa A Adamawa? - 3:42
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:42 0:00
Shiga Kai Tsaye
XS
SM
MD
LG