Masarautar Kano da gwamnatin jihar Kano sun dukufa wajen shirye-shiryen cikar Mai Martaba Sarkin Kano, Alhaji Ado Bayero shekaru 50 bisa gadon Sarauta.
A hirar da wakilinmu a Kano, Muhammad Salisu Rabiu ya yi da Mai Martaban, ya ce ya na mai matukar farin ciki da yadda jama'ar Kano ke cigaba da nuna masa kauna, duk da canje-canjen da zamani ya kawo. Ya ce Allah shi ke da zamani, saboda haka ya na mai na'am da duk wani sauyin da Allah ya kawo. Ya yi addu'ar Allah ya kawo zaman lafiya da cigaba ma Nijeriya.
Alhaji (Dr.) Ado Bayero ya zama Sarkin Kano na 13 a sarautar Fulani ranar 15 ga watan Yunin 1963.