WASHINGTON —
A yayin da arewacin Nijeriya ke cikin mawuyacin lokaci, a kuma daidai lokacin da zaben shugaban kasa na 2015 ke kara gabatowa, manyan kungiyoyin arewacin Nijeriya masu kama da juna wato kungiyar Tuntuba ta Dattawan Arewacin Nijeriya (ACF) da Kungiyar Dattawan Arewacin Nijeriya (NEF) sun kafa kwamitin hadin gwiwa saboda kawar da abin da su ka kira raba kawunan mutanen arewa.
A hira da ya yi da Ibrahim Ka-Almasih Garba na Sashin Hausa na Muryar Amurka, kakakin kungiyar ACF, Anthony Sani ya karyata rade-radin da ake cewa ana hada kai tsakanin ACF da NEF ne don zaben shugaban kasa na 2015. Ya ce kungiyoyi biyun sun yanke shawarar kafa kwamitin bai daya ne don su saka arewacin Nijeriya kan alkibla guda.
To saidai Sani ya ce kodayake ba su yin siyasar jam'iyya, dole ne su rinka yanke shawarwari masu nasaba da siyasa saboda su kare yankin na arewacin Nijeriya.