Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Jam’iyyun Adawa a Tanzaniya Sun Koka Kan Hana Su Shiga Zabe


Jam’iyyun adawa da dama a Tanzaniya sun koka cewa an hana daruruwan ‘yan takarar su shiga babban zaben da za'a gudanar a kasar.

Jam’iyyun adawa suna zargin cewa an hana daruruwan ‘yan takarar su shiga babban zaben ne wanda aka shirya za’a gudanar ranar 28 ga watan Oktoba a kasar.

Jam’iyyun sun yi kira da hukumar zabe ta magance koken na su, wanda suka mika a hukumance, bayan da kananan jami’an zaben suka cire ‘yan takarar majalisa da kansila da dama daga jam’iyyun adawa daga bisani jam’iyya mai mulki ta juyin juya hali, wacce aka fi sani da Chama Cha Mapinduzi.

Mataimakin Sakatare janar na babbar jam’iyyar adawa Chadema, Benson Kigaila, ya ce ‘yan takarar majalisar dokoki 57 da kansiloli 642 aka hana shiga zaben ya zuwa jiya Alhamis.

Kigaila ya bada labarin dan takara guda daya wanda ya nemi fom na daukaka kara. Maimakon haka, sai jami’in zaben ya rufe ofishin ya yi tafiyarsa. Dan takarar ya jira jami’in dukan yini amma bai dawo ba.

Kigaila ya bayyana cewa Chadema da wasu jam’iyyu biyu Civic United Front (CUF) da Wazalendo-Alliance for Change and Transparency ACT, sun kai kara wajen hukumar zabe ta kasa kuma suna kira da ayi bincike sosai don maida ‘yan takararsu, su tsaya zaben.

Dan takarar shugaban kasa a jam’iyar CUF, masanin tattalin arziki Farfesa Ibrahim Lipumba, ya fadi cewa jam’iyyarsa ta samu rahoton an kwacewa wasu ‘yan takara damarsu ta tsayawa zabe inda wasu da ba’a san ko su wanene ba suka sace musu fom.

" A kwai wasu da aka fid da su daga tsayawa bisa rashin cancanta.” A cewar Lipumba,

Da yake amsa tambayar wakilin VOA, Darektan Hukumar zabe yace Dr. Wilson Mahera Charles, Hukumar zaben ta karbi koken ‘yan adawar kuma tace zata yanke hukunci akan kowanne nan da shida ga watan Satumba.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG