Batun mutunta kason da dokokin kasa suka yi tanadi domin jinsin mata da nufin basu cikakkiyar damar shiga harakokin zabukan da ake shrin gudanarwa ta yadda zasu taka rawa sosai a harakokin gudanar da mulki na daga cikin muhimman batutuwan da taron na CNDP ya tattauna a kansu kamar yadda Dr Dita Idrissa kakakin kawancen MRN na jam’iyyu masu mulkin Nijer ya yi bayani.
Su ma dai jam’iyyu masu sassaucin ra’ayi da ake kira ‘yan baruwanmu sun yi na’am da wannan tsari na shigo da mata cikin sha’anin siyasa a fara daga batun basu tikitin zabe a cikin jam’iyyun siyasa, kamar yadda shugaban kawancen wadannan jam’iyyu, Malam Hambali Dodo ya bayyana.
Sake duba tsarin da ake gudanar da zabe a karkashinsa a Nijer na daga cikin bukatun da mahalarta wannan taro suka zo da su domin a cewarsu hanya ce da ka iya ba da damar dakile magudi sai dai wannan bukata ba ta sami shiga ba domin a cewar hukumar zabe dukkan wata kwaskwarimar doka a wannan lokaci da ake gab da soma fafatawa abu ne da ya sabawa doka.
‘yan adawa wadanda ke ci gaba da kauracewa dukkan wasu harakokin tsare tsaren zabe basu halarci wannan taro ba, matakin da ke nasaba da rashin halaccin da suka ce ya dabaibaye hukumar zabe ta CENI. A ranar 13 ga watan Disambar 2020 ne ake sa ran gudanar da zaben kananan hukumomi yayin da za a gudanar da zagayen farko na zaben shugaban kasa da na ‘yan majalisar dokoki bayan makwanni 2 kacal wato 27 ga wata.
Saurari cikakken Rahoton Souley Mumuni Barma.
Facebook Forum