Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Jam’iyyu 3 Cikin 5 Sun Musanta Amincewa Da ’Dan Takarar Shugaban Kasa Na PDP


Major Al-Mustapha
Major Al-Mustapha

Wata takaddama ce ke nemar kunno kai tsakanin Jam'iyyar adawa ta PDP da wasu Jam'iyyu uku, a karkashin jagorancin Jamiyyar AA, wato Action Alliance. Jam'iyyun da suka hada da APM da NRM sun karyata labarin da ke yawo game da kulla kawance da dan takarar Jam'iyyar PDP.

To saidai wani bincike da Muryar Amurka ta yi na nuna cewa wannan al'amari ya kawo rarrabuwar kawuna a jam'iyyun.

A wata sanarwa da ya fitar a Abuja, Shugaban wani bangare na Jam'iyyar AA wato Action Alliance, Adekunle Omo Aje ya ce jam'iyyar AA ba ta da irin wannan tsarin kuma ba ta shirin daukar wani mutum a madadin dan takararta na Shugaban Kasa. Adekunle ya ce bangaren Korarren shugaban AA Keneth Udezem tare da wasu jam'iyyu hudu ne suka ce sun amince da Atiku Abubakar na Jamiyyar PDP.

NRM NATIONAL RESVUE MOVEMENT PRO, ISMAIL ILIYASU ADAMU
NRM NATIONAL RESVUE MOVEMENT PRO, ISMAIL ILIYASU ADAMU

Manjo Hamza Al-Mustapha shi ne dan takarar Jamiyyar AA bangaren Adekunle Omo Aje, kuma ya yi tsokaci akan batun yana cewa har yanzu shi ne dan takara kuma Jam'iyyar AA dan takara daya ta ke da shi. Almustapha ya ce Suna da labarin abinda ya faru a Yola kuma nan ba da jimawa ba, za su tona asirin wadanda suka yi gaban kansu wajen daukar wannan mataki ba tare da umurnin Jam'iyya ba.

Shi ma Shugaban Jam'iyyar APM wato Allied Peoples Movement, Alhaji Mohammed Musa Bagana ya ce bangaren Jam'iyyar APM da shi yake shugabanta, ba ta shiga wata yarjejeniya da wata Jam'iyya ba.

Bagana ya ce tsohon shugaban Jam'iyyar wanda bai yarda cewa wa'adinsa ya cika ba, shi ne ya ke daukar irin wadannan matakai a madadin Jam'iyyar, kuma wadannan matakan ba sa kan doka. Bagana ya ce Jam'iyyar APM ta nesanta kanta daga matakin da tsohon shugaban APM ya dauka a Yola inda ya ce ya amince da dan takaran Jam'iyyar PDP, wannan ba da yawun uwar jam'iyyar ba ne.

A nashi jawabin a game da batun kawancen, mai magana da yawun Jam'iyyar NRM wato National Rescue Movement ta Kasa, Iliyasu Ismail Adamu, ya tabbatar wa Muryar Amurka cewa dama Jam'iyyar ta rabe gida biyu, saboda haka daya bangaren ce ta shiga yarjejeniya da PDP.

Ismail ya ce abin ya ba su mamaki a jam'iyyan ce, domin ba su amince da wanan mataki ba. Ismail ya ce jam'iyya ta lura cewa tsohon shugaban Jam'iyyar Isaac Udeh ne ya mika wuya a Yola. Ismail ya ce Jam'iyya za ta dauki mataki akan wadanda ke bata wa Jam'iyyar suna.

A nasa sharhi kan kamfen din PDP, mataimakin shugaban jam'iyyar na shiyar Arewa Umar Iliya Damagum ya ce dan takarar sa, Atiku Abubakar ya yi wa sauran zarra inda ya ce, Atiku ya fi su kwarewa, saboda haka wannan mataki ba zai hana Atiku cin Zabe ba.

Ba mamaki, a kwanakin karshe na makon zabe, akan samu wasu jam'iyyun na mara baya ga yan takarar da su ke ganin sun fi tagomashin lashe zabe.

Saurari rahoton:

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:57 0:00

XS
SM
MD
LG