Da yake tattaunawa da Sashen Hausa na Muryar Amurka, mukaddashin kakakin jam'iyyar APC na kasa, Mr. Yekini Nabena, ya ce abubuwan da ke faruwa a zahiri na nuna irin yadda Zamfara ke tallafawa ‘yan ta'addan da ke ci gaba da addabar arewa maso yamma.
Mr. Nabena ya ce alal misali ko daliban makarantar sakandaren kimiyya da ke Kankara da akai garkuwa da su Zamfara aka tafi da su, kana dukkan garkuwan da ake yi da mutane a Katsina can Zamfara ake kai mutanen, don ‘yan bindiga sunfi samun natsuwa da kwanciyar hankali a can.
Jam'iyyar APC ta ce idan akai la'akari da yadda gwamnatocin jihohin da ke makwabtaka da Zamfaran sukai watsi da shirin sulhu da ‘yan bindigar, amma a wannan lokaci gwamnatin Zamfara ke yin Afuwa ga ‘yan bindigar, wannan ya nuna akwai alaka tsakanin su.
Saboda haka, APC tayi gargadin cewa bai kamata a rinka yin siyasa da rayukan mutane ba, wanda ta nemi jami'an tsaro su binciki wannan batu.
Amma gwamnatin jihar Zamfara tayi watsi da wannan zargi inda ta ce baida tushe ballantana makama.
Kakakin gwamnan jihar Zamfara, Zailani Bappah, ya ce ai wannan batuma abin dariya ne, domin kuwa a zamanin da APC ke mulkin Zamfara ne akafi zubadda jinin bayin Allah da basusan hawaba basu san sauka ba.
Amma zuwan gwamna Matawalle an sami sauki sosai kuma wannan ya biyo bayan yin sulhu da ‘yan bindigar ne.
Ya ce idan ana batun gazawane to ai gwamnatin tarayya ke da sojoji, kuma dajin ba jihar Zamfara kadai ya tsaya ba, ya zagaye baki dayan shiyyar.
Saurari cikakken rahoton Hassan Maina Kaina:
Karin bayani akan: APC, Gwamna Mai Mala Buni, Buhari, da PDP.