BAUCHI, NIGERIA - Jakadan na kasar Sin, Mr. Cui Juan Chun, ya kai ziyarar aiki jihar Bauchi ne domin karfafa wasu kudurori guda biyar da ya tsara, da suka hada da farfado da masana’antu, ayyukan gona, sufuri da kuma batun tsaro.
Jakadan ya ce Najeriya da kasar Sin za suyi aiki tare, kan wadannan kudurori guda biyar don samar da muhimman kayayyakin inganta tattalin arziki, kimiyyar zamani, masana’antu da ayyukan gona.
Ya ce "ziyarar da na kawo jihar Bauchi, kyakkyawar manuniya ce, wadda za mu yi aiki tare da gwamnan jihar Bauchi. Ya ce mun gina hanyoyi, sannan muna da jari a fannin ayyukan gona, saboda haka akwai muhimmanci mu inganta cinikayya a kasashen biyu.
A nasa jawabin, Gwamnan Bauchi, Senata Bala Abdulkadir Muhammed, Kauran Bauchi, ya bayyana farin ciki da kuma jin dadi, kan ziyarar da Jakadan na kasar Sin ya kawo Jihar Bauchi.
Daga cikin kamfanonin da jakadan na Sin ya ziyarta har da kamfanin sarrafa shinkafa na Ti Amin, wanda yake da karfin sarrafa shinkafa har ton dari shida a kowace rana, zai kuma samar da ayyukan yi wa ‘yan kasa sama da dubu biyu.
Saurari rahoton daga Abdulwahab Muhammad: