BAUCHI, NIGERIA - A wata hira da Muryar Amurka, shugaban hukumar zabe mai zaman kanta a jihar Bauchi Alhaji Abdullahi Ibrahim, ya ce akwai katunan zabe da aka yi wa rijista sama da dubun sittin dake ofishin hukumar wadanda ba a karba ba.
Dan takarar kujerar gwamna a jam’iyyar APC a jihar Bauchi, Air Marshal Baba Sadik Abubakar mai ritaya, ya bukaci jama’a da su hanzarta zuwa karban katunansu.
Ya ce karbar katin zabe na da muhimmanci ga dimokardiyya saboda sai da shi za a iya kada kuri'a. A saboda haka ya zama wajibi wadanda suka canci kada kuri'a su karbi katinsu su kuma kare shi don tabbatar da cewa an yi adalci.
Alhaji Danladi Osi Kwano mai Warka-warka gogaggen dan siyasa ne, ya ce sama da kati dubu sittin ba karamar magana ba ce don duk wanda ya samu kuri'a dubu sittin zata iya yin tasiri gare shi.
Ya kara da nanata muhimmancin jama'a su je su karbi katunan zabensu. Idan ba ka da kuri'a ba ka da wani 'yanci, a cewarsa.
Saurari rahoto cikin sauti daga Abdulwahab Muhammad: