Matasan dai sanye da bakaken riguna sun mamaye ofishin samar da hasken wutar lantarki dake Minna, da kuma harabar majalisar Dokokin jahar. Inda suka ce idan har ba a sami canji ba nan da zuwa karshen wata zasu dauki mataki na mamaye madatsun ruwan guda Uku dake jahar.
Jagoran wannan zanga-zanga kwamarad Mohammad A Mohammad, yace sun fito ne domin nuna rashin jin dadinsu na kwashe shekaru biyu da watanni suna fama da rashin wuta. Wanda suke daura laifin kan kamfanin samar da hasken wutar lantarki na Abuja Electricity Distribution Company.
A cewar mallam Yahaya Mohammed Usman, yace a matsayin Jahar Neja ta inda ake samar da wutar lantarki, wadanda ke da Dam har guda Uku sai gashi sun kwashe kusan wata tara cikin duhu, wanda hakan yayi sanadiyar mutuwar kananan sana’o’i da dama.
Ko bayan kwalayen da ke dauke da rubuce rubucen nuna rashin jin dadi akan rashin wutar lantarkin, matasan na rera wakoki na nuna rashin jin dadi da yadda da rashin wutar.
Shugaban Majalisar Dokokin jahar Neja, Ahmad Marafa, yace zanga-zangar tayi dai dai alokacin da ya karbi bakuncin matasan a harabar Majalisar, inda yace bai kamata ba ace an rasa wutar lantarki a jahar Neja dake da Dam har Uku.
Domin karin bayani saurari rahotan Mustapha Nasiru Batsari.