Yau Laraba za a gabatar ma Shugaban Amurka Barack Obama cikakken jadawalin shirin yaki da mayakan kungiyar Daular Islama.
Shugaba Obama zai gana da Janar Lioyd Austin, Shugaban Sashin bayar da umarni ga sojojin Amurka, don su tattauna kan kokarin da ake kan yi, na hada kan kasashen duniya ta yadda za su iya fatattakar kungiyar Daular ta Islama, wadda ta kwace sassan Iraki da Syria, kamar yadda ya ke fata.
Shi ma Sakataren Tsaron Amurka Chuck Hagel zai shiga tattaunawar, kwana guda bayan da ya gaya wa wani Kwamitin 'yan Majalisar Tarayya cewa, wannan aikin na da sarkakkiya kuma zai dau lokaci. Ya kuma jaddada muhimmancin hada kai sosai.
Janar Martin Dempsey, Hafsan Hafsoshin sojojin Amurka, ya gaya ma wannan kwamitin cewa idan ya lura cewa akwai bukatar sojojin Amurka su mara ma na Iraki baya a wani fagen daga, zai nemi izini daga Mr. Obama.
Shugaban ya sha maimaita cewa ba zai tura sojojin yaki gadan-gadan zuwa Iraki ba.