A ranar Juma’a ne maharan a kan babura suka kai samame a Makarantar Sakandaren Kimiyya ta Gwamnatin ta 'yan maza inda suka yi musayar wuta da jami’an tsaro dake makarantar, lamarin da ya sa daruruwan dalibai suka arce daga makarantar suka boye a cikin jeji dake kusa da wurin.
Rahotanni sun nuna cewa, Gwamnan jihar Katsina, Aminu Masari, ya fada a jiya Lahadi cewa akwai dalibai kimanin 333 da ba a gano su ba bayan wata ganawa da jami’an tsaro. daliban makarantar sun kai 839.
A bangaren rundunar ‘yan sanda babu wani karin bayani tun bayan da ta ce an ceto dalibai 200 daga hannun maharan. Kakakin ‘yan sandan jihar Katsina SP Gambo Isah ya ce ana ci gaba da kai farmaki a cikin dazuka da hanyoyi da maharan kan yi amfani da su.
A halin da ake ciki kuma, iyayen yaran sun gudanar da zanga zangar lumana a garin Kankara suna kira ga gwamnati da ta ceto musu ‘ya’yansu daga hannun maharan. Wasu iyayen sun tattauna da Sashen Hausa yayin zanga zangar.
Abbas Mustapha Barde, yana cikin masu zanga zangar, ya kuma yi kira ga gwamnati da ta bi a hankali wajen bude wuta tsagaita kan maharan ta nemi hanya mafi inganci kuma marar hadari da zata karbo musu yara, Ya ce idan ba haka ba, a maimakon karbo yaran ina iya kashe su a musayar wuta. Barde ya shawarci iyayen daliban da su kara addu’a.
Wasu iyayen kuma sun bayyana damuwa a kan lamarin kana suka nemi gwamnati ta kara kaimi wurin ceto yaran. Sai dai iyayen sun ce babu wanda ya kira su domin neman kudin fansa kamar yanda aka saba gani a duk lokacin da aka sace mutane.
Ya zuwa yanzu babu wata kungiya ko wani mutum da ya dauki alhakin shirya wannan danyen aiki kamar yadda a baya kungiyar Boko Haram ta dauki alhakin yin garkuwa da ‘yan matan makarantar Chibok a arewa maso gabashin kasar.
Ga dai rahoton Sani Shuaibu Malumfashi daga Katsina:
Karin bayani akan: Tukur Yusuf Buratai, Buratai, sojoji, da jihar Katsina.