Gwamnan jahar Borno, Furfesa Babagana Umara Zulum ya ce a watan Janairun shekarar 2021 da ake dab da shiga, gwamnatin jahar Borno za ta bude dukkan hanyoyin da sojoji su ka rufe saboda tsaro. Hanyoyin sun hada da masu hada jahar ta Borno da wasu jahohin kasar da kuma masu hada wasu wuraren jahar da wasu.
An rufe wadannan hanyoyin ne tun shekaru da dama da su ka gabata saboda a samu kawo karshen matsalar tsaro a jahar, wanda har yanzu ba a samu yi ba kuma gashi katse hanyoyin na haddasa matsaloli iri iri ga rayuwar jama’a.
Gwamnan Zulum ya bayyana aniyar gwamnatin jahar ta sake bude wadannan hanyoyin ne a yayin gabatar da kasafin kudin shekarar 2021 a gaban Majalisar Dokokin Jahar Borno. Ya tabo batun tsaro sosai, inda ya hada da yankar ragon da aka yi ma wasu manoma sama da 40 kwanan nan a jahar.
Ga Haruna Dauda da cikakken rahoton: