Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Italiya Na Ci Gaba Da Daukan Tsauraran Matakai Akan 'Yan Cirani


Kwalwkwalwn 'yan cirani da suka makale a gabar tekun Italiya
Kwalwkwalwn 'yan cirani da suka makale a gabar tekun Italiya

Italiya ta kira kungiyoyin bada gaji na nahiyar Turai kada su taimaki kwale kwalen dake dauke da 'yan cirani fiye da 1000 da suka makale a gabar tekun kasarta

Kasar Italiya na ci gaba da daukan tsauraran matakai akan ‘yan cirani da suka makale a kan gabar tekunta, tana mai kira ga kungiyoyin nahiyar turai da ke ayyukan agaji, da su daina kubutar da ‘yan ciran, a maimakon haka, su rika bari jami’an tsaron gabar tekun Libya suna daukansu.

A jiya Lahadi, wata kungiya mai gudanar da ayyukan jin-kai a kasar Andalus ko kuma Spain da ake kira “Proactiva Open Arms” ta ce jami’an tsaron gabar tekun Italiya, sun samu sakon neman dauki daga kwalekwale shida da ke dauke da ‘yan cirani kusan 1000, amma kuma hukumomin Italiyan sun fadawa kungiyoyin jin-kan cewa ba a bukatar taimakonsu.

Yayin da hakan ke faruwa, shugabannin kasashen turai sun gaza cimma matsaya kan batun ‘yan cirani a wani dan karamin taron koli da suka yi a Brussels a jiya Lahadi.

Hakan kuma na nufin cewa, batun yiwuwar a cimma matsaya kan yadda za a tafiyar da kwararar ‘yan ciranin da masu neman mafaka, a taron da za su yi nan gaba a wannan mako, ya zama wani abu da kamar ba zai yiwu ba.

Amma duk da haka, wasu shugabanni a nahiyar, sun yi nasarar kai wa ga wani mataki na tunkarar batun ‘yan ciranin, da ya hada da kafa wata cibiya da za a rika karbar ‘yan ciranin, matsayar da Faransa da Spain suka amince da ita - duk da cewa kasar Italiya ta nemi da a yi garanbawul kan daukacin tsarin da nahiyar turai ke amfani da shi kan yadda ‘yan cirani ke shiga yankin.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG