Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ana Ci Gaba Da Zanga-zanga Akan Yadda Ake Tsare 'Yan Cirani a Amurka


Masu zanga zangar kin jinin yadda gwamnatin Trump ke tsare 'yan cirani tare da rabasu da 'ya'yansu
Masu zanga zangar kin jinin yadda gwamnatin Trump ke tsare 'yan cirani tare da rabasu da 'ya'yansu

Ana ci gaba da zanga zanga a jihar Texas saboda yadda aka tsare bakin haure da aka raba da 'ya'yansu kuma har yanzu babu wata hanya kwakwara da zasu sake haduwa da 'ya'yansu cikin sauki.

To a nan Amurka ma, ana ci gaba da zanga zanga kan yadda ake tafiyar da ‘yan ciranin da aka tsare a jihar Texas, wadanda suka shiga kasar ba bisa ka’ida ba, duk da cewa a ranar Laraba gwamnatin shugaba Trump ta sauya tsarin da take amfani da shi na raba ‘ya’ya da iyayensu akan iyakar kasar.

A jiya Lahadi, jami’an tsaron kan iyaka suka saki kimanin iyaye 30 da aka raba da ‘ya’yansu, an kuma fasa tuhumarsu saboda dokar da suka karya ta shiga kasar ba tare da izini ba.

Darektan kungiyar Annunciation da ke tallafawa bakin hauren, Ruben Garcia, ya ce, zabin da aka baiwa bakin hauren kan yadda za su samu bayanai game da ‘ya’yansu, bai taka kara ya karya ba, domin an ba su lambar 8-0-0 ce kawai domin tuntubar halin da suke ciki.

Wasu daga cikin iyayen, an tsare su ne a wani wuri da ke karamar hukumar El Paso a cewar Garcia.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG