‘Yan sanda sun ce, kamen na da nasaba da abubuwan da ke faruwa a ‘yan kwanakin a yammacin Gabar Kogin na Jordan, sai dai basu fayyace ko mutane nawa suka kama ba.
A daya bangaren, ma’aikatar tsaron kasar, ta bayyana cewa tana tsare da Meir Ettinger, wanda jika ne ga Malamin Bayahuden nan Meir Kahane da aka Haifa a Amurka, da kuma Eviatar Slonim, bayan da aka zarge su da alaka da kungiyoyo masu tsautsauran ra’ayi.
A dai makon da ya gabata aka kama mutanen biyu.
Ministan Tsaron kasar, Moshe Yaalon ya ba da umurnin a tsare wani mutum na uku mai tsautsauran ra’ayi a ranar Talatar da ta gabata.
Wannan kame ya biyo bayan wani hari da Yahudawa suka kai a ranar 31 ga watan Yulin da ya gabata a Yammacin Gabar Kogin Jordan, wanda ya halaka wani jariri Bafalasdine mai watannin 18 da mahaifinsa, kana ya kuma raunata mahaifiyarsa da dan uwansa.
Firai Ministan Isra’ila Benjamin Netanhayu ya kwatanta harin a matsayin aikin ta’addanci.