PM Isra’ila Benjamin Netanyahu ya yi kira ga shugaban yankin Falasdinu Mahmoud Abbas da ya ci gaba da shawarwari neman wanzarda zaman lafiya da suke yi, duk da cewa wa’din tsaida gine gine na kwariya kwariya a yammacin kogin Jordan na wata 10, da isra’ila ta dauka ya kare.
Jim kadan bayan karewar wa’adin ne shugaban Isra’ilan ya bada wata sanarwa a daren jiya lahadi yana kira ga Mr. Abbas ya ci gaba da shawarwarin domin cimma yar’jejeiya da ta zata zame abin tarihi cikin shekara guda. “Yace a shirye Isra’ila take ta ci gaba da tuntuba cikin kwanaki masu zuwa.”
Kamfanin dillancin labaran Faransa ya ambaci kakakin shugaba Abbas,Nabil Abu Rudeina yana cewa ta haka ne kadai shawarwarin wanzarda zaman lafiya zai sami nasara. Ya yi wan nan furucin ne daga birnin Paris inda Mr.Abbas yake ganawa da wakilan bani yahudu dake da zama a can a jiya lahadi.
Ahalin yanzu kuma wani jirgin ruwa dauke yahudawa ‘yan gwagwarmaya daga Isra’ila,da Turai,da Amurka sun kama hanya zuwa Gaza daga Cyprus da nufin karya killacewar da isra’ila ta yi wa yankin saboda su kai gudumawa. Jirgin mai tutar Ingila da ake kira Irene jiya lahadi ya tashi daga arewacin Cyprus dauke da fasinja tara da ma’aikatan jirgin.