Jami’an leken asirin kasashen Turai da kuma na Amurka sun bayyana cewa, sun bankado wata makarkashiyar kai harin ta’addanci a kasashen Biritaniya,da Faransa da kuma Jamus, watakil har da Amurka.
Jami’an dai basu yi Karin haske dangane da batun ba,sai dai kawai suka ce suna da tabbacin wannan makarkashiya. Rahotanni daga Amurka da kuma Birtaniya na nuni da cewa, ana niyyar kai hari ta’addanci ne irin wanda aka kai a Indiya cikin shekara ta dubu biyu da takwas, lokacin da wasu mayakan sakai masu da'awar kishin islama, suka kai hari kan wurare biyu a lokaci daya a Mumbai, da suka hada da otel din Taj.
Jami’an leken asiri sun sami labarin makarkashiyar kai harin ne a wurin wani dan asalin kasar Jamus da ake kyautata zaton dan ta’adda ne, wanda aka kama a cikin watan Yuli, da ahalin yanzu kuma yake hanun Amurka a Afghanistan.
An sami labarin makarkashiyar kai harin ne yayinda jami’an ‘yan sandan birnin Paris suka fitar da jama’a daga hasumiyar Eiffel jiya talata,a karo na biyu cikin wannan watan, sabili da barazanar ta’addanci. Ba a dai tarar da komi ba bayan an shafe sama da sa’oi biyu ana bincike.
Hukumomin kasar Faransa sun yi gargadi dangane da yiwuwar kai harin ta’addanci, sai dai babu tabbacin ko barazanar harin ta jiya Talata tana da nasaba da makarkashiyar kai harin ta’addancin da ake batu akai.