Firayim Ministan Isira’ila ya ce gwamnatinsa ta himmantu ga cimma yarjajjeniya da Falasdinawa wace za ta tabbatar da tsaro da kuma sauran muradun Isira’ilawa, to amman ya yi gum game da muhimmin batun nan na tsagaita gine-ginen matsugunan Yahudawa a Yamma da Kogin Jodan.
Benjamin Netanyahu ya yi wannan bayanin ne jiya Laraba bayan ganawarsa da Jakadan Amurka na Gabas Ta Tsakiya George Mitchell.
Kafin ganawar Mitchell y ace dama Amurka ta san cewa tattaunawar zaman zaman lafiyar za ta fuskanci cikas kala-kala, to amman wannan ba ya kashe wa Amurka gwiwa. Jakadan na Amurka ya koma Gabas ta Tsakiyar ce a wannan makon da niyyar shawo kan Isira’ila ta maido da dakatar da gine-ginen, wanda wa’adinsa ya cika ranar Lahadi.
Falasdinawa dai sun ce batun gine-gine a Yamma da Kogin Jodan din zai yi tasiri sosai kan ko za su ci gaba da tattaunawar ko a a. Babban mai wakiltar Falasdinawa a wurin tattaunawar Nabil Shaath ya gaya wa Muryar Amurka jiya Laraba cewa a halin yanzu Falasdinawa ba wai bukatar Isira’ila ta ruguza matsugunan su ke yi ba. To amman y ace bai kamata a cigaba da karfafa mamayar ba a sa’ilinda ake batun tattaunawar.