Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Isra'ilawa Sun Gudanar Da Zanga-Zanga Mafi Girma Tun Fara Yaki Don Kara Matsa Lamba Ma Netanyahu


Dubun dubatan Isra’ilawa ne suka yi dafifi a tsakiyar Birnin Kudus a zanga-zangar kin jinin gwamnati
Dubun dubatan Isra’ilawa ne suka yi dafifi a tsakiyar Birnin Kudus a zanga-zangar kin jinin gwamnati

Masu zanga-zangar sun bukaci gwamnati da ta cimma yarjejeniyar tsagaita bude wuta don kubutar da dimbin mutanen da mayakan Hamas suka yi garkuwa da su a Gaza da kuma gudanar da zabe da wuri.

Dubun dubatan Isra’ilawa ne suka yi dafifi a tsakiyar Birnin Kudus ranar Lahadi a zanga-zangar kin jinin gwamnati mafi girma tun bayan da kasar ta fara yaki a watan Oktoba.

Masu zanga-zangar sun bukaci gwamnati da ta cimma yarjejeniyar tsagaita bude wuta don kubutar da dimbin mutanen da mayakan Hamas suka yi garkuwa da su a Gaza da kuma gudanar da zabe da wuri.

ISRAEL-PALESTINIANS/POLITICS-PROTEST
ISRAEL-PALESTINIANS/POLITICS-PROTEST

Da farko dai al'ummar Isra'ila ta kasance cikin haɗin kai, kai tsaye bayan 7 ga Oktoba, lokacin da Hamas ta kashe mutane kusan 1,200 a wani harin da ta kai inda su ka yi garkuwa da wasu 250. Kusan watanni shida da aka kwashe ana rikici ya sake dawo da rarrabuwar kawuna dangane da shugabancin Firaiminista Benjamin Netanyahu, ko da yake yawancin 'yan kasar na goyon bayan yakin.

Netanyahu ya sha alwashin rusa Hamas tare da mayar da dukkan mutanen da aka yi garkuwa da su gida, amma haka ta kasa cimma ruwa. Yayin da Hamas ta sha asara mai yawa, har yanzu tana nan daram.

An sako kusan rabin mutanen da aka yi garkuwa da su a Gaza a cikin yarjejeniyar tsagaita bude wuta na mako guda a watan Nuwamba. Amma yunkurin da masu shiga tsakani na kasa da kasa suka yi na dawo da sauran wadanda aka yi garkuwa da su ya ci tura. An ci gaba da tattaunawa a ranar Lahadi ba tare da wata alama da ke nuna an cimma nasara ba.

Iyalan wadanda aka yi garkuwa da su suna ganin cewa lokaci ya kure, kuma suna kara nuna bacin ran su da Netanyahu.

"Mun yi imanin cewa babu wani wanda aka yi garkuwa da shi da zai dawo yayin wannan gwamnati saboda suna bata lokaci wajen tattaunawa na wadanda aka yi wa garkuwan," in ji Boaz Atzili, wanda aka yi garkuwa da dan uwansa, Aviv Atlizi da matarsa, Liat a ranar 7 ga Oktoba. An saki Liat amma an kashe Aviv, kuma gawarsa tana Gaza. "Netanyahu yana aiki ne kawai don son kansa."

Wasu na zarginsa da lalata dangantaka da Amurka, babbar kawar Isra'ila.

Netanyahu yana kuma fuskantar tuhume-tuhume na cin hanci da rashawa wanda sannu a hankali ke hanyar zuwa gaban kotuna, kuma masu sukar lamirin sun ce matakin nasa yana mai da hankali ne kan ci gaban siyasa a maimakon kan muradun kasa.

Yawancin iyalan wadanda aka yi garkuwa da su sun kaurace wa yin tir da Netanyahu a bainar jama'a don gujewa adawa da shugabancin da sanya lamarin masu garkuwar ya zama batun siyasa. Amma yayin da fushinsu ke karuwa, wasu a yanzu suna son canza matsaya - kuma sun taka muhimmiyar rawa a zanga-zangar adawa da gwamnati na ranar Lahadi.

Jama'a a ranar Lahadi sun baje kan shinge a kusa da Knesset, ko ginin majalisar, kuma masu shirya zanga-zangar sun sha alwashin ci gaba da zanga-zangar na kwanaki da dama. Sun bukaci gwamnati da ta gudanar da sabon zabe kusan shekaru biyu gabanin lokacin da aka tsara. Dubban mutane kuma sun gudanar da zanga-zanga a yau Lahadi a birnin Tel Aviv, inda aka yi wata gagarumar zanga-zanga a daren jiya.

Israel Palestinians
Israel Palestinians

A cikin jawabinsa na Lahadi, Netanyahu ya kuma sake nanata alkawarinsa na kai farmaki ta kasa a Rafah, da ke kudancin Gaza inda fiye da rabin al'ummar kasar miliyan 2.3 ke matsuguni bayan sun tsere daga fada daga wasu wuraren. "Babu wata nasarar da za a samu ba tare da shiga cikin Rafah ba," in ji shi, ya kara da cewa matsin lamba na Amurka ba zai hana shi ba. Sojojin Isra'ila sun ce mayakan Hamas sun ci gaba da zama a can.

Har ila yau a ranar ta Lahadi, wani harin sama da Isra'ila ta kai kan wani sansanin tanti da ke farfajiyar wani asibiti mai cike da cunkoson jama'a a tsakiyar Gaza, ya kashe Falasdinawa biyu tare da raunata wasu 15 ciki har da 'yan jarida da ke aiki a kusa.

Wani wakilin Kamfanin Dillancin Labarai na Associated Press ya dauki hoton harin da kuma abin da ya biyo baya a Asibitin Shahidai na Al-Aqsa da ke Deir al-Balah, inda dubban mutane suka fake. Rundunar sojin Isra'ila ta ce ta kai hari a cibiyar kwamandojin kungiyar 'yan ta'addar Jihadin.

Dubun dubatan mutane ne suka nemi matsuguni a asibitocin Gaza, inda su ke gani zai kare su daga hare-haren jiragen sama. Isra'ila na zargin Hamas da sauran mayakan da ke aiki a ciki da wajen cibiyoyin kiwon lafiya, abin da jami'an kiwon lafiya na Gaza suka musanta.

Sojojin Isra'ila sun shafe kusan makonni biyu suna kai farmaki a asibitin Shifa, asibit mafi girma a Gaza, kuma sun ce sun kashe mayakan da dama, ciki har da manyan jami'an Hamas. Ma'aikatar lafiya ta Gaza ta ce fiye da marasa lafiya 100 ne suka rage ba su da ruwan sha da kuma su ka raunuta, yayin da likitoci ke amfani da ledar roba a matsayin safar hannu.

Nan kusa da Asibitin Shifa da ke birnin Gaza, da dama daga cikin al’ummar tsirarun Falasdinawa Kirista na Gaza ne suka hallara a cocin Holy Family domin gudanar da bukukuwan Ista.

"Muna nan cikin bakin ciki," in ji mai halarta Winnie Tarazi. Kimanin mutane 600 ne suka fake a cikin harabar.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG