Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Isra’ila Da Hezbollah Na Fuskantar Caccaka Bisa Saba Yarjejeniyar Tsagaita Wuta


Yakin Isra'ila da Hamas
Yakin Isra'ila da Hamas

Daga Isra’ilan har kungiyar ta Hezbollah da Iran ke marawa baya na fuskantar caccaka game da karya alkawarin yarjejeniyar zaman lafiya da ta fara aiki a ranar 27 ga watan Nuwamba, da nufin kawo karshen yakin da ake yi.

A ranar Asabar ma’aikatar lafiyar Lebanon tace, wani harin da Isra’ila ta kai ta sama ya kashe mutane 6 a yankin kudancin kasar, kwanaki 10 da kulla yarjejeniyar tsagaita wuta tsakanin kungiyar Hezbollah da Isra’ila.

Daga Isra’ilan har kungiyar ta Hezbollah da Iran ke marawa baya na fuskantar caccaka game da karya alkawarin yarjejeniyar zaman lafiya da ta fara aiki a ranar 27 ga watan Nuwamba, da nufin kawo karshen yakin da ya lakume rayukan dubbai a Lebanon, ya kuma tarwatsa dimbin mutane da ga sassan biyu.

Wata sanarwa da ta fito daga ma’aikatar lafiya tace, mutane biyar ne su ka yi shahada, wasu biyar suka jikkata sakamakon hari ta sama da Isra’ilan ta kai kan birnin Beit Lif, hakazalika, a wani harin na dabam, wani harin jirgi mara matuki ya kashe mutum guda a yankin Deir Seyan.

Wuraren biyu na da nisan kilomita 20, wato mill biyu tsakanin juna.

Tun da farko a rannar Asabar, sojojin Isra’ila suka ce, sun kai hari kan mayakan Hezbollah a kudancin Lebanon, wanda daya ne daga hare haren da ta ke kai mata, kan abinda ta kira barazana ga Isra’ila.

Sojojin Isra’ilan sun kara da cewa, a daya da ga cikin hare haren, sojoji sun gane wani mayakin Hezbollah da ya kasance barazana ga dakarun da aka girke a kudancin Lebanon, wanda hakan ya sabawa yarjejeniyar tsagaita wutar da aka kulla, inda da ga nan ne dakarun sama suka bude mu su wuta.

Kafar yada labarum kasar Lebanon ta ruwaito cewa, wani jirgin sama mara matuki na makiya, ya kaikaici wani babur a Deir Seryan.

Ko a ranar Litinin sai da ma’aikatar lafiyar tace, wani hari ta sama da Isra’ila ta kai ya hallaka mutane 9 har lahira a kudancin Lebanon, bayan da Isra’ilan tace, tana kaikaitar wasu gwamman wurare ne na Hezbollah a matsayin ramuwar gayya na wani hari da mayakan Hezbollah din su ka dauki alhakin kai shi.

A ranar Laraba, sakataren harkokin wajen Amurka Antony Blinken yace, za’a cigbaba da yarjejeniyar tsagaita wutar, duk kuwa da abubuwan da suka faru marasa dadi.

An dorawa wani kwamiti da ya kunshi Faransa, jami’an wanzar da zaman lafiya na Majalisar Dinkin Duniya, Isra’ila da Lebanon, da Amurka ta jagoranta, alhakin tabbatar da dorewar tattaunawa tsakanin bangarori dabam dabam, da tabbatar da gano duk wata cin amana ko karan tsaye ga yarjejeniyar, da yin maganin ta, domin kaucewa zurfafar rikicin.

Piraiministan Lebanon Najib Mikati yayi kira ga al’ummar duniya, musamman bangarorin da ke daukar nauyin tsare tsaren tsaro, da su yi aiki tukuru bisa hangen nesa na ganin an taka birki ga karya ka’ida daga abokan gaba, tabbatar da janyewar su daga wuraren da suka mamaye, da ba da gudummuwa haikan domin tabbatar da tsagaita wuta.

Hare haren da Isra’ila ta kai Gaza ya kashe akallah Palasdinawa 34 a ranar Asabar, cewar jami’an lafiya a yankin, a daidai lokacin da Qatar ta bayyana fatan ganin sabon fadi tashin ya kai ga cimma samar da yarjejeniyar tsagaita wuta tsakanin Isra’ila da Hamas.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG