Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Wasu Gwamnonin Amurka Suna Turjiya da Karbar 'Yan Gudun Hijiran Syria


Shugaban Amurka Barack Obama
Shugaban Amurka Barack Obama

Yayinda shugaba Obama ke shirin bada izinin karbar 'yan gudun hijira dubu goma daga kasar Syria wasu gwamnonin kasar sun nuna kin karbar 'yan gudun hijira a jihohinsu saboda da harin Paris kasar Faransa

Akalla gwamnoni daga jihohin Amurka 10 ne suka bayyana turjiya kan karbar 'yan gudun hijira daga Syria, bayan harin da aka kai kan birnin Paris, a dai dai lokacinda shugaba Obama yake fada jiya Litinin cewa, bashi da niyyar tsaida shirin karbar 'yan gudun hijira dubu 10 daga kasar Syriar da yaki ya daidaita.

Hukumomi a Turai sun gano cewa akalla daya daga cikin maharan da suka farwa birnin Paris ranar Jumma'a, ya sulale ya shiga Turai tsakanin dubban 'yan gudun hijira da suke gudu daga yakin basasar da kasar Syria take fama da shi.

Shugaba Obama ya fada a wani taro da manema labarai a Turkiyya cewa, Amurka ba zata kyale wani dan gudun hijira daga Syria ya shiga Amurka ba, sai bayan an gudanar da binciken kwa-kwab ta fuskar tsaro akansa.

Ya kara da cewa "kin karbarsu zai kasance cin amanar manufofi da muradun Amurka. Mr. Obama yace "abun kunya ne, kuma sabanin halin Amurka" ne shawarar da wani dan takarar shugaban kasa karkashin jam'iyyar Republican Senata Ted Cruz ya bayar, cewa Amurka ta karbi 'yan gudun hijira Kiristoci daga Syria kadai , amma banda Musulmi.

XS
SM
MD
LG