A taron masu ruwa da tsaki akan dabarun shugabanci da aka gudanar a birnin Jos jihar Filato, mahalarta taron sun bayyana cewa kowa na da gudunmuwar da zai bayar wajen ci gaban kasa.
Mr. Cletus Akhimen, shugaban kamfanin COA media, shine ya shirya taron ya kuma ce Najeriya na da dimbin albarkatu amma rashin shugabanci na gari shi ke sa rashin ci gaba a kasar.
Alhaji Sani Mu’azu, dake shugaban ma’aikatar Lenscope media kuma ke harkar fina-finai, ya gabatar da kasida a wurin taron inda ya bada shawara akan a bude kafofin da matasa zasu sami hanyoyin inganta rayuwarsu.
Shabul Mazadu, na daya daga cikin wadanda suka halarci taron yace sai shugabanni sun maida hankali wajen tallafawa al’umma kafin a sami ci gaba a jihar Filato da kasa baki daya.
Shi kuma mai ba gwamnan jihar Filato shawara akan harkokin kungiyoyi masu zaman kansu, Irmiya Sauni Werr ya yi kira ga al’umma akan su ba shugabanni goyon baya don su iya aiwatar da kudurori masu kyau.
Saurari cikakken rahoton Zainab Babaji daga Jos:
Facebook Forum