Jam’iyar PDP mai adawa a Najeriya, na ci gaba da kalubalnatar shugabancin shugabar rikon kwaryar hukumar zaben Najeriya ta INEC, Hajiya Amina Zakari, tana mai zargin cewa nada ta da aka yi yunkuri ne na tafka magudi a zaben jahohin Kogi da Bayelsa.
Wadannan kalamai na zuwa ne yayin da Zakari ta kara fayyace manufofin aikinta inda ta ce za ta ci gaba da amfani da na’urar tantance masu kada kuri’a domin yin maganin masu yunkurin yin magudi.
Sai dai PDP, ta ce za su iya bakin kokarinsu suga cewa sun hana jam’iya mai ci ta APC cimma burinta da PDP ta ce tana yi domin mai da Najeriya kasa mai jam’iya daya.
“Mun sha alwashin cewa za mu hana jam’iyar APC cimma burinta na mayar da Najeriya kasa mai jam’iya guda.” In ji Kakakin PDP Oliseh Metuh.
Ana ta bangaren, dan takara a karkashin jam'iyar APC a zaben cike gurbin dan majalisa a jahar ta Katsina, Hassan Kabiru 'Yar'adua, ya ce korafe-korafen da PDP ke yi ihu ne bayan hari.
"Amina Zakari ba ita ce za ta gudanar da zabe ba, INEC ce za ta gudanar da zabe wadda ta kasance ta na guanadar da zabuka a baya."
Wanna takadamma na ci gaba da kunno kai ne yayin da hukumar ta INEC ke shirin gudanar da zaben cike gurbin dan majalisar tarayya a jahar Katsina a watan gobe da kuma zabukan gwamnoni a jahohin Kogi da Bayelsa da za a yi a watannin Nuwamba da Disamba.
Wannan ba shi ne karon farko da jam'iyar ta PDP ke kiran a cire Zakari ba, jim kadana bayan nada a kan wannan mukamin bayan Farfesa Attahiru Jega ya kammala wa'adinsa, PDP ta nuna rashin amincewarta da zabin.
Ga karin bayani a rahoton wakilin Muryar Amurka, Nasiru Adamu El Hikaya: