Najeriya ta shiga matsalar tattalin arziki saboda kudin shiganta wanda akasari na fitowa ne daga bangaren man fetur ya yi karanci saboda kasuwar man fetur ta fadi.
Masanin tattalin arziki Shu’aibu Idris ya gaya ma abokin aikinmu Ladan Ibarhim Ayawa cewa tun shekaru 13 zuwa 15 da su ka gabata, a zamanin Shugaba Olusegun Obasanjo, aka bayyana ma Najeriya cewa Amurka ta gano wata hanyar samun mai, kuma muddun ta habbaka ta, za ta rage sayen man Najeriya. Ya ce tun sannan aka gaya ma Najeriya ta fara shiri saboda ta iya tsayawa da gindinta idan Amurka ta habbaka hanyar samun man.
Ya ce saboda haka ne ma Obasanjo ya bullo da wani asusun rarar kudin man fetur wanda ake kira “excess crude account” inda har aka yi ajiya a kasar waje wanda ake kira “foreign reserve” ta yadda har wani lokaci kudin ya kai Naira Biliyan 67. Y ace to amma bayan gwamnatin Obasanjo sai aka yi ta rarraba kudaden a gwamnatin marigayi Umar ‘Yar’Adua da kuma gwamnatin Goodluck Jonathan aka yi ta kashewa barkatai. Y ace a baya can ana sai da mai akan dala 110 ganga guda, amma yau ana sai da shi ne akan dala 55.
Da Ladan ya tambaye shi ko akwai wata mafita ga Najeriya, sai ya ce akwai mafita amma kuma mai wuyar bi. Ya ce farashin mai ko dala 70 da kyar ya kai. Karshenta ma in ji shi, farashin na iya raguwa zuwa dala 40 koma dala 30. Ya ce abin da zai dada rage farashin mai shi ne dawowar hulda tsakanin Amurka da Iran. Y ace abin da zai taimaki Najeriya kawai shi ne gwamnati ta gari da aka samu da kuma kwato kudaden da aka sace da gwamnati mai ci din ta kuduri aniyar yi.