DIFFA, NIGER - Shekaru kusan bakwai kenan da matasan jihar Diffa suka rungumi sana’ar farauta ta amfani da karnuka fiye da hamsin a mota daya, al’amarin da ya fara kawo karancin wasu dabbobin dawa, musamman barewa da zomo.
Daya daga cikin mafarautan da ya nemi a sakaya sunansa ya bayyana cewa sukan yi gayya su kuma dauki hayar mota don zuwa farauta da karnuka kimanin hamsin zuwa saba'in.
A yanzu haka jami’an da ke kula da kare gandun daji na jihar Diffa sun fara daukar matakan ladabtarwa ga matasan da ke gudanar da farautar ba kan ka’ida ba.
Mamman Laminou, shi ne mataikamakin babban darektan kula da kare gandun daji na jihar Diffa, ya ce yadda ake farautar yanzu ya saba wa doka. Ya kara da jan hankalin jama’a da su yi hattara.
Ita ma kungiyar mafarautan gargajiya ta jihar Diffa ta kalubalanci yadda sannu a hankali matasan jihar suka fara amfani da hanyoyin zamani wajen gudanar da farauta.
Matasan na jihar Diffa sun bayyana cewa farautar ita kadai ce madogara a gare su saboda ba su da wata sana’ar yi, kuma daukar mataki a kansu wata hanya ce ta kara samun masu zaman kashe wando ga matasa a jihar ta Diffa, da a yanzu haka ke fama da matsalar tsaro.
Saurari cikakken rahoton Aboukar Issa: