Mutane goma sha biyu ne suka mutu wasu da dama kuma suka jikata a lokacin da wani direba ya shiga da motarsa cikin taron jama a kasuwar sayen kayan bukin Krismeti.
Wata takardan sammaci daga hukumomin Jamus ta ayyana wani dan shekaru 24 a matsayin wanda ake tuhuma mai suna Anis Amri dan garin Ghaza a kasar Tunisia, mai tsayin mita 1.78 mai bakin gashi da kuma idanunsa nada launin rawaya.
Rahotannin kafofin watsa labarai sun ce da yammacin jiya Laraba yansanda sun kai samame a cikin wani gini a Lardin Kreuzburg a cikin Jihar Berlin suna farautar Amri amma basu same shi ba.
A can kasar Tunisia kuma mahaifin Amri yace dansa ya bar gida zuwa Turai shekaru bakwai da suka shude kuma an tsareshi a kasar Italy kafin ya wuce zuwa kasar Jamus.
A wata sabuwa kuma shugaban Amurka mai jiran gado Donald Trump ya fada a jiya Laraba cewa hare haren ta’addanci da ake kaiwa a Turai a cikin wannan mako yana tabbatar da maganarsa cewar idan ya kama aiki a wata mai zuwa zai sa a tantance duk wani musulmi dake niyar shigowa Amurka.
Trump yace kowa ya san niyarsa kuma maganarsa na kara tabbata dari bisa dari a kullu yaumi. Da yake wata ganawa da yan jarida a Florida inda yake ci gaba da yiwa jami’an gwamnatinsa tambayoyi, Trump yace abinda ya faru wani abin kunya ne.