Gwamna Rotimi Amaechi na Jihar Rivers a kudancin Najeriya, zai gana da masanin harkar kwamfuta, kuma mai bayar da agaji, Bill Gates, domin tattauna zuba jari a fannin ayyukan kiwon lafiyar jama'a.
Shugabar Kungiyar Rigakafi ta Duniya da ake kira "Global Alliance on Vaccines and Immunization" ko kuma GAVI a takaice, Violaine Mitchell, ta ce Mr. Gates, wanda shi ne shugaban Gidauniyar Bill da Melinda Gates, yana dokin ganawa da gwamnan na Jihar Rivers domin tattauna muhimman batutuwa a fannin kiwon lafiya da raya kasa.
Ms. Mitchell ta yi bayanin cewa samun nasarar kawar da cutar shan inna ko Polio daga Najeriya, ya dogara a kan gwamnonin jihohin kasar, kuma duk abinda zai faru a cikin Najeriya zai shafi yadda za a yaki wannan cuta a sauran duniya. Ta ce lakanin kawar da cutar shi ne ci gaba da aiwatar da shirin rigakafi.
Gwamna Amaechi ya amsa da cewa kudurinsu shi en na tabbatar da cewa an samu nasara mai yawa wajen yakar cutar shan inna ko polio nan da karshen wannan shekara. Ya tabbatar da cewa shi ma yana dokin ganawa da Mr. Gates.
Gwamnan na Jihar Rivers ya ce gwamnati tana da likitoci 200 wadanda ta rarraba zuwa asibitocinta domin cimma nasarar shirin rage yawan mace-macen uwaye mata da kuma jariran da suke haifa.