Mutanen da aka kama suna da masaniya cewa jami’ar Northern New Jersey bata da malamai, ko azuzuwa, ko kwasa kwasan bada digirori, amma basu san cewa, ma’aikatar tsaron cikin gida ta Amurka ce ta kafa jami’ar ba.
An kirkiro da jami’ar a shekara ta dubu biyu da goma sha biyu da cikakken shafin sadarwar internet da alkawarin aiwatar da tsarin ilimantarwa na dabam, a yunkurin ma’aikatar tsaron cikin gidan na dakile cuwa cuwar takardun VISA A Amurka.
Lauyan gwamnatin jihar New Jersey Paul Fisherman ya shaidawa manema labarai cewa, dillalan VISA da masu daukan dalibai suna tururuwa zuwa jami’ar bogin lokacin da batun ya fita fili wani ya shaidawa Fisherman cewa, an dade ana cuwa cuwar, “wata sabuwar hanyar ziyarar share wuri-zauna".
An tuhumi mutanen ishirin da daya da suka shiga hannu, wadanda galibi suke da izinin zama Amurka, da laifin hada baki da nufin aikata zamba a tsarin VISA da kuma hada baki su nemi kudi ta wajen tsugunar da bakin haure.
Galibin ‘yan kasashen ketaren da suka ci moriyar cuwa cuwar, sun fito ne daga kasashen India da kuma China, kuma sun riga sun shigo Amurka da takardar VISA ta yawon bude ido, amma suke neman hanyar zama din din din. An gano su kuma hukumomin shige da fice zasu dauki mataki a kansu, amma ba za a tuhumesu ba, inji Fisherman.
Jami’an gwamnati sun shaidawa jaridar New York Times cewa, yanzu haka dai, galibin dalibai miliyan daya da dubu dari biyu da ke Amurka da takardar VISAr dalibai suna jami’oin na zahiri.
An bada rahotannin keta dokar VISA a duk fadin Amurka, abinda yasa jami’an shige da fici kara daukar matakin tantance masu neman takardun VISA da nufin tabbatar da cewa basu da alaka da ta’addanci.