Jiya Litinin John Kerry ya yi wannan furucin bayan da ya gana da takwaran aikinsa na Turkiya Mevlut Cavusoglu.
John Kerry yace kasashen biyu suna da sha'awar ganin bayan 'yan kungiyar ISIS cikin gaggawa domin maida zaman lafiya da kwanciyar hankali a yankin.
Kasar Turkiya kawar kungiyar kawancen tsaron NATO ce. Tana cikin wani bangaren sojojin kawancen taron dangi dake fafatawa da 'yan yakin sa kai na kungiyar ISIS a kasashen Iraqi da Syria.
To saidai duk da haka Amurka da Turkiya suna da sabani akan goyon bayan da Amurka ke baiwa 'yan yakin sa kai na Kurdawa da Turkiya ta ce suna da alaka da kungiyar Kurdistan Workers' Party ko PKK a takaice, wata kungiyar 'yan ta'ada da take yakin samun 'yancin cin gashin kai daga kasar Turkiya