Binciken da lauyan gwamnati ya gudanar akan wata badakalar biliyon ko milliard 8 na cfa da ake zargin wani ma’aikacin fadar shugaban kasa Ibrahim Amadou ‘’Ibou Karaje’’ da handamewa ne ya bada damar gano wasu wadanda ake zargi da taka rawa wajen fitar da wadanan kudade daga asusun bital malin kasa. bayan shafe wunin laraba ya na sauraren wadanan jami’an ma’aikatar kudi alkali ya kulle mutane 12 a ci gaba da bincike matakin da shugaban kungiyar transaparency Maman wada yace ya yi dai dai.
Yanzu haka wannan batu ya dauki hankalin masu amfani da kafafen sada zumunta inda mahawara ta kankama a tsakanin masu kare gwamnati da wadanda ke ganin ba za a rasa hannun wasu manyan kusoshin jam’iyar PNDS mai mulkito amma wani jigo a jam’iyar Adamou Manzo na danganta abin da yunkuri irin na masu neman haddasa rudani.
A na sa ra’ayin kakakin jam’iyar RDR Canji ta ‘yan adawa Alhaji Doudou Rahama kwatowa kasa hakkinta daga hannun mahandama cikin yanayin adalci shi ne abinda ‘yan hamayya ke jira daga mahukunta.
A washegarin darewarsa karagar mulki ne shugaban kasa Mohamed Bazoum ya umurci ministan shara’a ya dauki matakin damkawa mashara’anta wasu takardun binciken da hukumar yaki da cin hanci Halcia ta gudanar a fadar shugaban kasa abinda ya bada damar gano wani jami’in fadar wato Ibarhim AmadouIbou Karaje da wawure makuddan miliyon cfa da yake cirowa daga asusun bital malin kasa ta hanyar amfani da takardun bogi lamarin .
Saurari cikakken rahoton cikin sauti: