Lamarin da ya faru ne a yayin da suke zagaya birnin Yamai da nufin fadakar da jama’a akan muhimmancin ranar ‘yancin dan adam ta duniya da ake bukukuwanta a ranar 9 ga watan Disamban kowace shekara matakin da uwar kungiyar ta kasa ke kallo a matsayin wata alamar koma bayan dimokradiya a kasar ta Nijar.
Jami’an fafitikar da suka fada hannun ‘yan sanda a yayin wannan zagaye na raya ranar ‘yancin dan adam sun hada da mukarraban kungiyar Tournons La page na gundumomi 4 na birnin Yamai da wani bafaranshen dake wakiltar cibiyar uwar kungiyar Tournons la Page a Nijer kamar yadda shugaban kungiyar na kasa Maikol Zody ya bayyana a taron manema labarai
Kungiyar ta koka akan matakin hana wa magoya bayanta gudanar da zanga zanga a wasu jihohi a yau lahadi da nufin nuna bukatar ficewa sojojin Faransa daga Nijar.
Kawo yanzu mahukunta ba su bayyana dalilan kama jami’an na kungiyar Tournons La Page ba, kuma a makon jiya ma kungiyar ta janye zanga zangar da ta shirya gudnarwa a ranar Lahadin da ta gabata bayan da kotun daukaka kara ta birnin Yamai ta ba hukumomi gaskiya a shara’ar da aka shafe ranakun Juma’a da Asabar a na tafkawa a tsakanin bangarorin biyu.
Hakan na zuwa ne bayan da magajin garin Yamai ya hana ‘yan fafitika fitowa kan titi da nufin gwada bukatar ficewar sojojin Barkhane daga Nijer.
Saurari cikakken rahoton cikin sauti: