A Faransa, wani kakakin gwamnatin kasar ya fada yau Laraba cewa mutumin da ya kai hari kan wani dan sanda a Paris da guduma a Notre Dame Cathedral, wani dalibi ne da ke karatu a matakin digirinsa na uku, kuma ya ba ya zargin an sauya mai tunani zuwa na mai tsatsauran ra’ayi.
A wata hira da aka yi da Christoper Castener a gidan radiyon RTL, Kakakin gwmanati ya ce ‘yan sanda sun saka harin a jerin na ta’addanci saboda furucin da mutumin ya yi a lokacin harin.
Collomb har ila yau ya fadawa manema labarai cewa wani katin shaida da aka samu a jikin maharin ya nuna cewa mutumin dalibi ne dan asalin kasar Algeria.
Sannan wani bincike da ‘yan sanda suka gudanar a gidansa ya gano wani faifain bidiyo da mutumin ya yi na mubaya’a ga kungiyar IS.
Shi dai maharin ya sulalo ne ta bayan wasu ‘yan sanda uku dake sintiri da rana, yayin da masu yawon bude ido suka yi cincirindo a bakin Notre Dame.
Facebook Forum