Biyo bayan kokarin cibiyoyin Majalisar Dinkin Duniya ke yi, suma kungiyoyin agaji na ‘kasa da ‘kasa da ma hukumomi a Najeriya sun tashi tsaye, inda yanzu haka sami raguwar mace mace tsakanin ‘kananan yara a sansanonin ‘yan gudun hijira dake shiyyar Arewa maso Gabashin kasar.
A baya dai Majalisar Dinkin Duniya ta yi gargadin cewar kimanin kananan yara 500,000 zasu iya rasa rayukansu samakanon karancin abinci mai gina jiki. Hakan yasa hukumar kula da yara ta UNICEF ta tunkari matsalar gadan gadan.
A wata hira da Muryar Amurka ta yi da jagoran aikace-aikace na hukumar UNICEF, yace suna mayar da hankali sosai a kan kananan yara ‘yan ‘kasa da shekaru biyar, bayan an ware su ana kuma gudanar da gwaje gwaje a kansu domin tantace wadan ke fama da cutar yunwa da kuma wanda basa fama da wannan matsala. Haka kuma ana baiwa yaran abinci mai gina jiki, da kuma sauran kayayyakin da suke bukata.
Saurari rahotan Hassan Maina Kaina daga Abuja.