Hukumar lafiya ta Duniya WHO, ta nuna damuwa kan yadda hukumomin Tanzania suke jan kafa, wajen fitar da bayanai kan zargin bullar cutar Ebola a kasar, inda ta yi kira da su fito karara su sanar da duniya halin da ake ciki.
Makonnin biyu da suka gabata, hukumar lafiyar ta samu wani rahoto wanda aka fitar da shi ba a hukumance ba, da ke nuna cewa wani mutum mai shekaru 27 ya mutu sanadiyyar cutar da ake tunanin ta Ebola ce a Dar el salam, babban birnin kasar.
Fadela Chaib, ita ce mai magana da yawun hukumar ta WHO.
Ta kuma kara da cewa, duk da nacin da suka nuna wa kasar ta Tanzania na su fitar da bayanai, har yanzu shiru kake ji.
A dai ranar 14 ga watan nan na Satumba, hukumomin na Tanzania suka kira wani taron manema labarai, inda suka musanta bullar cutar a kasar.
Facebook Forum