Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Hukumar Kwallon Kafar Burundi Na Ci Gaba Da Shirye-shiryen Gasar Zakaru


Hukumar kwallon kafa ta kasar Burundi na ci gaba da shirin gasar zakarun kasar duk da mummunan hadarin dake tattare da yaduwar cutar coronavirus a kasashen duniya.

A wannan makon, kasar dake gabashin Afirka ta sanar da cewa a karon farko an tabbatar mutane uku sun kamu da cutar COVID-19.

Duk da cewa mutane kalilan ne suka kamu da cutar a Burundi, har yanzu hukumomin kasar basu dauki matakan kariya don tunkarar cutar ba, ta hanyar haramta manyan tarukan jama'a.

Mai horar da kungiyar kwallon kafa ta Vital’O FC, Jean Gilbert Kanyenkore, ya ce 'yan wasan suna daukar matakai kamar wanke hannayensu da kuma gaisawa ba tare da shan hannu ba.

Ana kuma gwada zafin jikin ‘yan kallo dake isa filin wasan, don a tantance ko suna fama da zazzabi ko, alamar dake nuna mutum na dauke da kwayar cutar.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG