Hukumar kiwon lafiya ta duniya ko WHO a takaice tace an tsaida da yaduwar cutar Ebola a Najeriya da Senegal, kodashike yawan wadand cutar ta hallaka a yammacin Afirka ya zarce dubu biyu da dari takwas.
Wani rahoto daga ofishin hukumar a shiyyar Afirka yace ba a sami sabbin mutane da suka kamau da cutar ba a Najeriya tun ranar takwas ga wannan wata, a Senegal ba'a sake samun wani da ya kamu da cutar ba bayan mutum daya tilo da aka bada rahoto akansa ranar 29 ga watan Agusta.
Rahoton yace kusan za’a ce baki daya an dakila yaduwar cutar a wadannan kasashe biyu”.
A wani rahoton hukumar na daban, WHO’n tace a kasashen Guinea da Laberiya da Saliyo ana samun sabbin mutane da cutar take kamawa. Rahoton yace yawan mutane da suka kamu da cutar ya haura zuwa dubu biyar da dari takwas da sittin da hudu, yayinda Ebolan ta hallaka mutane dubu biyu da dari takws da goma sha daya.
Hukumar tace wata annoba ta daban ta barke a Jamhuriyar Demokuradiyyar Kwango, har mutane 71 suka harbu 40 kuma suka mutu dalilin haka.