Sai dai masu ruwa da tsaki na ganin batun kidaya ba shi ne abinda ke damun jama'a ba, tunda an yi sheharu 15 ana amfani da jadawalin kidayar da aka yi a baya kuma babu abinda ya canza.
A wata ganawa ta musamman da shugaban Hukumar Kidayar Jama'a ta Kasa Nasir Isa Kwarra yayi da yan jaridu a Abuja, yayi bayani cewa a yanzu haka hukumar ta riga ta tura ma'aikatan ta fili suna kokarin kasafta kasar zuwa gundumomi wato abinda ake kira EAD ko Eumeration Area Demarcation a turanci.
Nasir Isa ya ce an sauya fasalin yin aikin yanzu inda mutum biyu kacal suke aikin kuma zai dauke su kwanaki biyu ne ko uku.domin akwai na'ura da ke dauke da unguwa baki daya da kuma hoton gidajen da lambobi gidajen, sannan a sanya tambayoyi da masu gida za su amsa su aiko shi ta na'ura zuwa shalkwata Hukumar.
Amma ga Kwararre a fanin zamantakewan dan Adam, Abubakar Aliyu Umar ya nua damuwarsa da fargaba da kuma tsaro inda ya ce kamata ya yi mahukunta su yi la'akari da halin rashin tsaro da kasa ke ciki, ga bala'i na fatara da yunwa da ke addabar mutane, sai a ce za a fitar da mukudan kudade wai saboda kidaya? Ya ce a hakura a cigaba da amfani da jadawalin da ake ta amfani da shi shekaru 15 da suka wuce har sai hankalin yan kasa ya kwanta.
Shugaban Komitin Kula da Harkar Kidayar Jama'a a Majalisar Wakilai Mohammed Lawal Idris ya bada tabbaci cewa yin wannan kidaya a shekara 2022 wajibi ne, domin zai tabbatar da yawan jama'ar kasa da kuma sanin baki wadanda ba yan kasa ba ne. Mohammed lawal ya ce babu kasar da ke zaune kara zube ba tare da ta san yawan al'umman ta ba, ta yaya za ta yi tsari da zai shafe su? Hasali ma yana ganin mutane na tsoron batun za6e ne da za a yi a shekara 2023, kuma yana ganin ba zai shafi zabe ba tunda har sai an gama kidaya har na tsawon shekara daya kafin a yi zabe.
Lawal Idris ya bada shawara cewa mutane su yi tawakali, saboda duk abinda mutum yayi dole ne akwai abin dubawa na ko a yi nasara ko kuma hatsari ya auku ko kuma a gama lafiya. Saboda haka abu ne mai kyau kasa ta san yawan adadin jama'ar ta duk da korafe korafe da ake yi.
Abin jira a gani shi ne yadda wanan aiki zai yi tasiri a magance kalubalen da ya gabata a Najeriya a shekarun baya da aka yi kidaya, domin kasar ta samu nasarar sanin yawan jama'ar ta.
Saurari cikakken rahoton cikin sauti: