Hukumar kidayar jama’a, ta Najeriya, tace an samu raguwar mutuwar mata wajen haihuwa, a jihar Neja.
A lokacin mika rahoton wani bincike da hukumar kidayar jama’a, tayi akan batun mace-macen mata, a wurin haihuwa, a cikin shekaru biyu da suka gabata, hukumar tayi na'am da sakamakon binciken.
Hukimar kidayar ta ce duk da yake har yanzu akwai sauran aiki, amma mutuwar matan a wurin haihuwa, ya ragu da kashi 63 a cikin 100, a jihar ta Neja.
Shugaban hukumar kidayar jama’a, na Najeriya, mai kula da jihar ta Neja, Barrister Umaru Datti, yace an samu gagarumin nasara idan aka kwatanta da shekarun baya.