Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Wasu 'Yan Kabilar Tibi Sun Zargi Sojoji Da Cin Zarafin Iyalansu


Yayin da rundunar sojin Najeriya ta tura jami'anta wasu yankunan kudancin jihar Taraba a arewa maso gabashin kasar don yaki da bata gari, yanzu kuma an soma ce-ce-ku-ce a tsakanin shugabanin al'ummar kabilar Tibi da sojojin bisa zargin wuce gona da iri da kuma cin zarafin jama'a.

Shugabanin kabilar Tibi sun zargi jami'an sojin da keta hurumin iyalansu ta hanyar kone-kone da kuma fyade, batun da shelkwatar tsaron ke cewa za ta yi bincike a kai.

A wani taron manema labarai da hadakar kungiyar al'ummar kabilar Tibi ta Najeriya ta kira, shugabanin kabilar sun ce a wani samame da sojoji suka kai a wasu sassan kudancin jihar Taraba sun ci zarafin iyalansu da kuma kai farmaki ga wadanda ba su ji ba, ba su gani ba.

A bayanin da ya yi, shugaban kungiyar al'ummar Tibi Chief Goodman Dahida, ya zargi sojojin da wuce gona da iri a wani farmaki da suka kai a ranar 29 ga watan Yuni, a kauyukan Tse Juku da Akinde da ke karamar hukumar Donga.

A martanin da shelkwatar tsaron Najeriya ta fitar da ke dauke da sa hannun babban jami'in kula da harkokin yada labaran shelkwatar Manjo Janar John Enenche, rundunar sojin ta musanta zargin da al'ummar Tibin ke yi.

Manjo Janar John Enenche ya ce sojojin na da kwarewa, don haka bai ga makama a zargin da ake yi ba, amma ya bada tabbacin cewa rundunar sojin za ta yi bincike akan lamarin.

Mallam Musa Jika na kungiyar Amnesty Support Group, wanda har ila yau ke cikin wakilai da kuma ‘yan sa ido na kungiyar kare hakkin bil Adama, ya yi kira da a gudanar da kyakkyawan bincike.

Saurari karin bayani cikin sauti.

please wait

No media source currently available

0:00 0:04:09 0:00


Facebook Forum

XS
SM
MD
LG