Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Hukumar Farin Kaya Ta Shigar Da Kara Kan Tsohon Shugaban Babban Bankin Najeriya, Emefiele


Tsohon Shugaban Babban Bankin Najeriya CBN, Godwin Emefiele
Tsohon Shugaban Babban Bankin Najeriya CBN, Godwin Emefiele

Hukumar tsaron farin kaya ta Najeriya, DSS, ta ce ta shigar da kara a gaban kotu tana tuhumar gwamnan babban bankin kasar Godwin Emefiele da aka dakatar, biyo bayan umarnin da kotu ta bayar tun farko cewa, ko dai a gurfanar da shi ko kuma a sake shi.

WASHINGTON, D.C - Takardu da lauyoyin gwamnati suka shigar sun nuna cewa Emefiele na fuskantar tuhumar laifuka da suka hada da karkatar da kudade, wanda ke nufin zai iya fuskantar dauri mai tsawo a gidan yari idan aka same shi da laifi

Hukumar ta DSS ba ta bayar da cikakken bayani kan tuhumar da ake yi masa ba, kuma a yanzu Emefiele bai gurfana a gaban kotu ba.

A ranar 9 ga watan Yuni ne sabon shugaban kasa Bola Tinubu ya dakatar da Emefiele daga kan aiki, sannan kuma bayan kwana guda hukumar DSS ta kama shi.

Hukumar ta DSS ta fada a sanarwar cewa, “bayan umarnin wata babbar kotun Abuja a ranar, 13 ga Yuli, 2023, ma’aikatar harkokin gwamnati ta tabbatar da cewa an gurfanar da Godwin Emefiele a gaban kotu bisa bin umarni ne.”

Za a mika takardun na kotu ga lauyoyin Emefiele, sannan kotun za ta sanya ranar da za a gurfanar da shi, inda a lokacin ne za a bukaci ya amsa ko kuma kin amsa aikata laifin..

Shugaba Tinubu ne ya bayar da umarnin dakatar da aikin sa, kasa da makonni biyu da hawansa mulki. Ba da jimawa ba, babban bankin ya dage takunkumin da ya sanyawa kasuwancin domin daitaita harkokin bankin ta yadda za a samu masu sa hannun jari daga kasashen waje.

Sharrudan kundin tsarin mulki na Najeriya ya hana a tsare mutum na sa’o’i fiye da 48 ba tare da shigar da gurfanar da shi a kotu ba.

Saidai lauyoyin gwamnati sun ce sun samu umarni ne daga karamar kotun majistare da a ci gaba da rike Emefiele na tsawon lokaci yayin da ake ci gaba da bincike.

Emefiele, wanda tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari ya nada a karo na biyu Lokacin mulki sa na shekaru biyar a shekarar 2019, zai yi ritaya a shekara mai zuwa. Buhari ya goyi bayan karfafa kudin kasar wanda ya ke gani a matsayin wani abin alfaharin ga kasar.

-Reuters

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG