Wannan batu dai ya sake kunno kai ne a daidai lokacin da wasu ‘yan Najeriya ke ci gaba da yin korafe-korafe a game da yadda ba sa iya samun adadin takardun kudin da suke bukata a zahiri a bankunan kasuwancin kasar baya ga matsalar na’ura da sabis-sabis mai inganci wajen tura ko karbar kudi ta intanet ko manhajojin bankunan da ake yawaitar fama da su.
A hirar ta da Muryar Amurka, Ambassada Khadija Ishaq Bawas, ta bayyana cewa, ta shafe sama da watanni biyu bata rike tsabar kudi a hannunta. Bisa ga cewarta,
marin ya yi muni ainun da tilas idan mutum yana son ko da takardun kudi na Naira 200 ne, sai mutum ya dora lada a kai.
A bayaninsa, babban Bankin Najeriya ta bakin darakta mai lura da harkokin bankuna na bankin, Malam Haruna Bala Mustapha, yace Bankin na ci gaba da buga sabbin takardun kudi tare da rarraba tsoffin kudin don a samu wadata a kasar yana mai cewa wasu ‘yan kasar idan suka sami sabbin tsakardun kudi suna ajiyewa ne don gudun abun da ka je ya dawo nan gaba kuma nan bada jimawa ba za’a samu saukin al’amarin sossai.
Idan Ana iya tunawa dai a ranar 3 ga watan Maris ne kotun kolin Najeriya ta yanke hukuncin tsawaita wa’adin amfani da takardun Naira dari 2, dari 5 da ma dubu 1 zuwa ranar 31 ga watan Disambar shekarar 2023 bayan kwan-gaba kwan-baya da aka yi ta samu da matakin janye tsoffin takardun kudin daga cikin alumma tun karshen watanJjanairun lamarin da ya jefa mutane cikin matsatsin rayuwa.
A Saurari cikaken rahoton Halima Abdulra'uf: